Cigiyar Musulunci Ta Al Azhar ta yi tir da Allah wadai da harin ta'addanci da aka kai a kasuwar Madagali Arewa maso Gabashin Najeriya

  • | Thursday, 15 December, 2016
Cigiyar Musulunci Ta Al Azhar ta yi tir da Allah wadai da harin ta'addanci da aka kai a kasuwar Madagali Arewa maso Gabashin Najeriya

Cibiyar Musulunci ta Al Azhar al- Sharif ta yi Allah wadai da kazamin harin ta'addanci da wasu 'yan mata 'yan kunar bakin wake na kungiyar Boko Haram su biyu suka kai a wata kasuwa da take cike da jama'a a garin Madagali Arewa maso Gabashin Najeriya, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane alkalla 30, da kuma jikkata mutane masu yawa...

Cibiyar ta Al Azhar tana kara tabbatar da cewa ire iren wadannan ayyuka na ta'addanci sun yi hannun riga da karantarwar addinai gaba daya, kamar yadda suka saba da dukan al'adun mutunta ka, tana kuma kara bayyana cewa irin yanda kungiyar take amfani da 'yan mata wajen zartad da hare hare akan fararen hulan da ba su ji ba ba su gani ba babban dalili ne da yake nuna irin yanda kungiyar suka yi nesa da dabi'un tausayi da jinkai da kuma tsarin zamantakewa, kafin ma su yi nesa da karantarwar addinin Musulunci da rangwamen sa.

A daidai wannan lokaci da Cibiyar AL Azhar take tir da Allah wadai da wannan hari na ta'addanci, tana kuma kaddamar da ta'aziyya ga 'yan uwa da iyalan wadanda harin ya ritsa da su, tana kuma rokon Allah ya bai wa wadanda suka jikkata lafiya na gaggawa...

 

Print
Tags:
Rate this article:
4.0

Please login or register to post comments.